Labarai
Ganduje na kokarin karama Sarki Aminu Karfin Iko…
Gwamna ganduje ya nemi Majalisar jihar Kano ta canja tsarin dokar mulkin sarakunan jihar Kano, idan baku manta dai tsarin masarutun guda biyar ya kasance akwai Shugaban Majalisar sarakunan Wanda dokar ta bayarda damar shekaru Bibiyu ga duk wanda ya jagoranci Majalisar, yanzu ganduje ya nemi Majalisar data canja tsarin dokar ya zamana duk wani Wanda ya kasance sarkin tsakiyar birni to shine zai jagoranci Majalisar sarakunan na har’abada, yanzu idan wannan doka ta tabbata Aminu Ado bayero sarkin Kano shine zai jagoranci Majalisar sarakunan ta jihar Kano na tsawon rayuwarsa…