Ganduje ne ke daukar nauyin korarrun ‘yan jam’iyar NNPP domin su Kori Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir ~Cewar Jam’iyar NNPP.

Uwar jam’iyar NNPP ta Kasa tace Mun samu labari cewa wasu korarrun ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da suka hada da Tope Aluko da wasu tsofaffin shugabannin jihohi, wadanda ake daukar nauyinsu, suna gudanar da taron manema labarai a Jabi, Abuja suna bayyana karya a matsayin farfaganda, cewa Gwamnan jihar Kano H.E. Abba Kabir Yusuf bai kasance dan jam’iyyar NNPP ba kamar a lokacin zaben kuma an kori mai girma Sanata Rabi’u Kwankwaso daga jam’iyyar.
Wadannan zarge-zarge kwata-kwata karya ne kuma kuskure ne. Mun bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano ya kasance dan jam’iyyar NNPP mai gaskiya a kowane lokaci kuma muna da yakinin Kotun Koli ta Najeriya za ta yi adalci. Wadannan hmutane da aka yi hayar su wanda ake zaton fitowarsu daga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Ganduje, da alama sun sayar da ransu, kuma za su yi duk wani abu da za su yi don samun riba ta hanyar cin gajiyar zaben Najeriya.
Muna tunatar da jama’a cewa Cif Boniface Aniebonam daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar NNPP a kwanakin baya ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya bukaci a tabbatar da zabensa. Don haka abin mamaki ne yadda wasu daga cikin masu biyayyarsa za su yi kasa a gwiwa har su zama Yan haya domin suyi wa ’yan Najeriya mummunar karya.
A karshe muna kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da maganganun karya na wadannan makiya tsarin zaben Najeriya!