Addini

Ganduje Ya Bai Wa Ma’aikatan Kano Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis a matsayin ranar hutun ma’aikata a jihar albarkacin ranar ɗaya ga watan sabuwar shekarar Musulunci ta 1442.

A jiya Talata ne Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ta fitar da sanarwa tana umartar al’ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Muharram a daren yau Laraba, wanda shi ne watan farko a kalandar Musulunci.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, Fadar Gwamnatin Kano ta ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci mazauna jihar da su yi amfani da hutun domin yi wa Kano addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.

Kazalika gwamnan ya buƙaci mutane “su ji tsoron Allah a harkokinsu na yau da kullum domin samun sauƙi game da wahalhalun tattalin arziki da ake ciki” sannan kuma su zauna lafiya da juna.

Bisa tsarin kalandar Musulunci, idan an ga watan a daren Laraba to Alhamis ce ranar ɗaya ga sabuwar shekarar. Idan ba a gani ba kuma, za a cika watan Zul Hijja kwana 30 – watan ƙarshe – sai Juma’a ta zama ranar sabuwar shekara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button