Ganduje ya cire mu a Apc mu Kuma mun cire shi daga tsarin siyasar Kano na har abada ~Cewar Abdulmimin Jibrin kofa

Mai magana da yawun jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Abdulmumin Jibrin, ya ce da yawa daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kora daga jam’iyyar sun koya masa darasi na siyasa a rayuwarsa.
Idan dai za a iya tunawa, a tunkarar zaben 2023, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama sun fice daga jam’iyyar zuwa NNPP.
Jam’iyyar NNPP ta doke jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris bayan lashe mafi yawan kujerun majalisun tarayya da na jihohi.
Mista Jibrin, wanda zababben dan majalisar wakilai ne a karkashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin gidan talabijin na Channel TV mai suna ‘Politics Today’.
Ya ce: “A koyaushe akwai irin wannan alaka, da kuma dadewar alaka da shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso, wanda a zahiri ya kai ni siyasa.