Siyasa

Ganduje Ya Kafa Kwamiti Don Bincikar Kwankwaso.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Gwamnatin jihar Kano, karkashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kaddamar da kwamitin da zai binciki ayyukan ginda titina 5k dake fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

An bada aikin gina titunanne a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso. Mun kawo muku cewa gwamnatin Kano ta sokenaikin titin 5k dake Dawakin Tofa saboda barin aikin da aka yi ba tare da kammalashi ba.

Dalilin hakane ma gwamnatin ta kafa kwamiti dan bincikar irin wadannan ayyuka a sauran kanan hukumomin jihar dan tabbatar da yanda suke, kamar yanda kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya bayyana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button