Ganduje Ya nemi Alkali yayi gyara a Bilyan uku 3bn na Shari’arsa ja’afar ja’afar kan bidiyon Dollars.
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, ya nemi gyara a jerin masu ikirarin shaidu a karar sa da jaridar DAILY NIGERIAN da ma wallafin ta, Jaafar Jaafar.
Gwamna Ganduje ya maka Jaafar a gaban kotu, yana neman a biya shi diyyar N3billion Sakamakon wallafa bidiyon gwamnan na cusa dala a aljihunsa.
Tun a ranar 10 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne, Gwamna Ganduje ya gabatar da bukatar a gaban lauyoyinsa domin neman umarnin gabatar da karin bayanan shaidun.
A zaman da aka ci gaba a ranar Alhamis, Lauyan Mista Jaafar, Ubi Eteng, ya nuna rashin amincewa ga bukatar a kan cewa cin zarafin hanyoyin kotu ne.
Amma, lauyan Mista Ganduje, MN Duru, ya dage cewa an kawo karar a karkashin tsari na 24, dokoki na 1, 2 da 3 na babbar kotun farar hula da ke jihar 2014.
Alkalin da ke sauraran shari’ar, Mai Shari’a Suleiman Namalam, ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga Maris don yanke hukunci da ci gaba da sauraro bayan zafafan mahawara.