Ganduje ya sake rage albashin ma’aikata daga N30,000 Zuwa N18,000 mafi karancin albashi.
Gwamnatin Kano ta dakatar da biyan dubu talatin N30,000 mafi karancin albashi ga ma’aikatanta, inda ta koma N18,000 – wanda shi ne na baya.
Bayan matsin lamba daga kungiyoyin kwadago, Shugaba Muhammadu Buhari a watan Afrilu 2019 ya sanya hannu kan sabon dokar mafi karancin albashi zuwa doka, wacce ta tanadi N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.
A watan Disambar 2019, gwamnatin Kano ta amince da fara biyan ma’aikatanta sabon mafi karancin albashin, yayin da za a sasanta basussukan watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2019 kashi-kashi.
Amma Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun Gwamna Dr Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar, ya shaida wa Jaridar TheCable cewa saboda koma bayan tattalin arziki da cutar ta COVID-19 ta haifar, jihar ba zata iya ci gaba da biyan N30,000. Ba.
“Gwamnatin jihar ta koma kan mafi karancin albashinta na farko saboda koma bayan tattalin arziki. Yakasai yace Abin da muke samu yanzu a matsayinmu na gwamnati ya ragu, kuma ba za mu iya biyan N30,000 mafi karancin albashi ba, ”inji shi.
Bayanai daga ma’aikatan gwamnati sun ce gwamnati ba ta sanar da su ci gaban ba.
“Mun ga ragin a cikin watan Nuwamba da kuma na Disamba, kuma ba wanda ya gaya mana komai,” in ji wata majiya, ta kara da cewa: “Su ma ‘yan fansho sun rage a cikin kudinsu kuma ba a ba da dalilin hakan ba.
Cutar ta COVID-19 da ta zama annoba ta shafi tattalin arzikin Najeriya.