Labarai

Ganduje yana fuskantar zargin satar takin zamani, hatsi, da motocin noma da aka siyo domin rabawa manoman Kano na biliyoyin naira

Spread the love

Sabbin binciken na iya kara tsananta kan gwamnatin Abdullahi Ganduje na aikata laifuka, wanda ya hada da bidiyon cin hanci da rashawa na shekarar 2018.

Jami’an yaki da cin hanci da rashawa a Kano sun sanar da cewa gano tarin takin zamani da hatsi da kayan noma da aka sace a wani dakin ajiyar sirri na jihar.

Hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC) ta ce jami’anta na binciken yadda aka sace sama da Naira biliyan 4 da aka kashe wajen sayo kayayyakin da aka boye a wani dakin ajiyar kaya a karamar hukumar Kumbotso.

Jami’ai sun gano manyan motocin Toyota Hilux, manyan motoci, taraktoci, buhunan siminti, takin zamani, tayoyi, waken soya, da masara da dai sauransu, a lokacin da suka kai samame a wani kauye mai nisan kilomita 30 a kudu maso gabashin Birnin Kano.

Hukumar ta PCACC, wacce a farkon wannan watan ta kaddamar da bincike kan faifan bidiyon na Mista Ganduje na dalar Amurka, yanzu haka ta tsare tare da cafke akalla mutane biyar masu alaka da ma’ajiyar, kamar yadda wata majiya a PCACC ta bayyanawa wakilinmu.

“Tsohon gwamna Ganduje na da alaka da wannan zamba,” in ji wani jami’in.

Mista Ganduje, gwamnan Kano daga Mayu 2015 zuwa Mayu 2023, ya yi kaurin suna a cikin jerin faifan bidiyo da wata jaridar Najeriya, Daily Nigerian ta fitar, a shekarar 2018 inda ya ke karbar ‘dala’.

Gwamnan ya musanta kuma ya yi barazanar kai karar mawallafin sa.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar dai ta ce ta gayyaci tsohon gwamnan da ya gurfana a gaban hukumar kan lamarin, wanda ta ce hakan ya biyo bayan tantance bidiyon da aka yi kuma aka tabbatar da sahihancin sa.

A baya dai hukumar ta kama Idris Saleh, tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa wanda ya yi aiki a karkashin gwamnatin Ganduje bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.

Muhuyi Magaji, shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa na Kano, ya zayyana wasu daga cikin kayayyakin da aka kwace daga rumbun ajiyar ga manema labarai jim kadan bayan kammala aikin a ranar Asabar.

Jami’ai sun ce wadanda aka kama kan haramtattun kaya na da alaka da Mista Ganduje, wadanda wasu daga cikinsu sun karbi kudade daga asusun gwamnati a lokacin gwamnatin Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button