Ilimi

Ganduje Zai Dauki Malamai Alarammomi Aikin Koyar Da Yara A Jihar Kano.

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya amince da daukar Alaramma sittin (60) a matsayin Malamai da zasu karantar da dalibai a sabbin makarantun Almajirai da ya gina guda 15 a cikin jihar Kano.

Gwamnan ya bayar da wannan amincewar ne biyo bayan tattaunawa da Kwamitin Gudanar da Makarantun Alqur’ani da Islamiyya na Jihar Kano ya gabatar ta hannun Kwamishinan Ilimi Mal. Muhammad Sanusi Kiru a wannan rana.

Aikin ya kara nuna kyakkyawan kokari na gwamnan Kano wajen kawar da matsalar barace-barace da kuma samar da makarantu na Allo a cikin jihar tare da samar da kayan aikin yau da kullun kamar su gidajen kwana, da kuma ingantaccen tsarin karatun da zai baiwa Almajiri Yara damar haddace Alkur’ani mai girma da kuma samun ilimi na zamani a cikin kyakkyawan tsari da aminci.

Dangane da wannan ci gaba, za’a gabatar da Alaramma 60 na makarantu guda uku (3) na sabbin makarantun Almajiri da ke Bunkure, Kanwa a Madobi da Kiyawa a karamar hukumar Bagwai bandasu za’a gina a kowacce karamar hukuma.

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button