Rahotanni

Ganduje Zai Kaddamar da Kwamitin Mika Mulki Mai Mambobi 17

Spread the love

Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata da misalin karfe biyu na rana a dakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano.

Majalisar zartaswa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje a jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mika mulki mai mambobi 17 domin mikawa gwamnatin jihar Kano mai jiran gado.

Majalisar ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mutum 100 wanda za a fitar da kundin tsarin mulki daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban (MDAs).

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba, wanda ya ne ya bayyana wannan batu a lokacin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar da aka yi na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce ana sa ran zababben gwamna Abba Yusuf zai bada wakilai uku ga babban kwamitin.

Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin jituwa da nufin rubutawa tare da mika rahoton mika mulki na karshe cikin makonni uku.

Ya ce kwamitin zai kuma samu tare da tantance rahotanni daga MDAs dangane da manyan nasarorin da aka samu, gami da ayyuka/tsari da ke gudana dangane da matakin aiwatar da kasafin kudi, matsaloli, takurawa da dai sauransu daga ranar 25 ga Mayu zuwa yau.

Kwamishinan ya bayyana cewa an ba wa babban kwamitin rikon kwarya umarnin fara shirin mika mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki biyu na gwamnatin Ganduje.

Ya ce Ganduje zai kaddamar da kwamitin ne a ranar Talata da karfe 2 na rana a dakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano.

Da yake magana game da kafa kwamitin, Garba ya ce, “Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji yana da kamar haka shugaban ma’aikatan gwamnati, babban lauya/Kwamishanan shari’a, kwamishinan, watsa Labarai, Kwamishinan Muhalli, Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Haɗin kai.

“Sauran su ne kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, kwamishinan kananan hukumomi, kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, kwamishinan kudi, kwamishinan ilimi, babban darakta, ofishin kula da filaye, darakta-janar, bincike da takardu, Manajan Darakta, Tsare-tsaren Birane. da Hukumar Raya Kasa, yayin da Babban Sakatare, Bincike da Harkokin Siyasa, REPA za ta zama sakataren kwamitin.

Garba ya yi nuni da cewa, an dora wa kwamitin alhakin daidaitawa tare da saukaka ayyukan karamin kwamitin kan mika mulki, tattarawa da hada rahotonsu tare da rubutawa da mika rahoton mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin makonni hudu bayan kaddamar da shi.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a cikin wa’adin da aka kayyade don baiwa gwamnatin da ke kan karagar mulki damar taka rawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button