Labarai
Ganduje zai kashema kanawa bilyan uku 3bn

Gwabnan Jahar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakane A gurin bikin fara gabatar da rigakafin cutar maleriya da akayi A fadar masarautar bichi Ajiya
Gwabnan yace kudin hadin gwaiwa ne tsakanin Gwabnatin Kano da kungiyar yaki da cutar maleriya ta duniya
Ganduje yace wanan Shirin yazama dole sakamakon yadda cutar maleriya take kashe yara da mata ajahar Kano inda yace za’a gudanar da rigakafin a daukacin kananan hukomomin jahar Kano 44
Bikin kaddamar da rigakafin ya samu halartar matemakin Gwabnan Kano Dakta Nasir yusif Gawuna da Mai martaba sarkin Bichi Alh nasiru Ado bayero da kwamishinan lafiya na jahar Kano Dakta Aminu Ibrahim tsanyawa da sauran manyan mukarabban Gwabnati Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano