Rahotanni

Ganduje zai mika mulki ga Abba a yau domin halartar bikin rantsar da Tinubu

Spread the love

A yau ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje zai mika ragamar mulki ga zababben gwamnan jihar, Abba Yusuf a hukumance.

A ranar 29 ga watan Mayu ne dai za a rantsar da dukkan wadanda aka zaba.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar ranar Lahadi, ya ce ana gudanar da taron ne da misalin karfe 9 na dare a gidan gwamnati dake Kano.

Garba ya ce kwamitin mika mulki na gwamnatin jihar ya sanar da ci gaban ga kwamitin mika mulki na zababben gwamnan jihar.

Ya ce kwamitocin biyu sun gana ne a cikin mako guda inda aka gabatar da takardar mika mulki ga kwamitin zababben gwamnan tare da tsara wata manufa da ta dace da bikin.

Kwamishinan ya bayyana cewa bayan taron, Ganduje zai tashi zuwa Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano don kaddamar da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, ranar Litinin.

Ya kara da cewa tafiyar gwamnan ya zama dole domin cimma cikar wa’adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe Internation Airport, Abuja, domin kaddamar da shugaban kasa.

Garba ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button