Ganin Kimar Shugaba Buhari da Gwamnatinsa ne Ya Hanani Zuwa Kotu~Ibrahim Magu

Jaridar Sahara Reforters ta Rawaito Cewa- Dakataccen Mukaddashin shugaban yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati da Zagon Kasa EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa zai bada cikakken hadin kai wajan binciken da ake masa.
Yace kuma baya tunanin kai gwamnatin shugaban kasa Buhari kotu saboda yana ganin kimar shugaban kasar kuma shima yana daga Cikin wani Bangarene na gwamnatin.
Magu ya shafe kwanaki 10 a tsare yayin da kwamitin da shugaban kasa ya kafa ke bincikensa da Laifin Wawushe dukiyar da ya karba a Hannun Barayin Gwamnati.
Da yake magana ta bakin Lauyansa, Wahab Shitu, Magu yace har yanzu ba’a gabatar masa da laifukan da ake zarginshi da su a hukumance ba amma duk da haka wadanda yake gani a shafukan sada zumunta zai mayar da martani akansu.
Yace ba zai shiga cikin bata gwamnatin shugaban kasar da ake ba kuma zai bada hadin kai a bincikeshi saboda ya yadda babu wanda yafi karfin Doka Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas