Kasuwanci

Gas Shine Makomar Najeriya, Inji Shugaban Kamfanin NNPC Kyari

Daraktan kula da Kamfanin NNPC, Mele Kyari ya ce iskar gas ce makomar cigaban makamashi a Najeriya.

Kyari wanda yake magana a yayin taron kungiyar makamashi Seplat 2020 wanda aka gudanar a Legas, ya ce Afirka musamman Najeriya tana da albarkatun gas wanda za a iya amfani da shi tare da ba da dama ga sauran damar.

An shirya babban taron tare da taken “Dorewa a Kan Kasuwanci da jagoranci a Afirka” don jawo hankali ga manyan dama da gas ke bayarwa.

A cewar Kyari, “Dole ne mu manta da cewa duniya na canji zuwa makamashi mai sabuntawa, kuma gas ne makomar.

Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, da ire-iren su da kungiyoyin sa-kai, da shugabannin kasuwar hada-hadar kudade, da ‘yan kasuwar mai da gas, masu saka hannun jari, masu ba da shawara, shugabannin zartarwa, masana tattalin arziki, manazarta, da kamfanoni masu zaman kansu.

Shugabar kungiyar Gas a Najeriya, Audrey Joe-Ezigbo a cikin gudummawar ta ta ce, “Muna da bukatar yin amfani da kudin Afirka sama da tiriliyan 527 wanda aka tabbatar da ajiyar Gas sannan mu yi amfani da wannan bangaren ta hanyar inganta ayyukanmu na sabuntawa wanda ya kamata Najeriya ta zama mai nasara. “

Shugaban kamfanin Seplat, Ambrosie Orjiako ya ce kamfanin zai ci gaba da kasancewa mai bibiyar lamarin yayin da yanayin kasuwancin yake canzawa, yana mai cewa “kasuwancin mai na Seplat zai zama babban matakin farko na tabbatar da cewa ayyukanmu sun yi daidai da labarin canjin yanayi.”

Babban jami’in shigowa
na Seplat, Roger Brown, ya ce Afirka a matsayin wata nahiya na bukatar gina wannan tushe wanda zai iya ginawa da kuma jigilar iskar gas wanda Najeriya zata iya jagoranta ta hanyar samar da makamashi mai sabuntawa.

Dangane da tsammani daga gwamnati wanda zai ba Najeriya damar taka rawa, Brown ya ce ya kamata gwamnati ta tallafawa kamfanonin mai ta hanyar hada gwiwa a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa, da karin tallafi a gasa da hada-hadar amincewa da kuma ingantattun dokoki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button