Tsaro

GASKIYA BA SASANCI AKAI DA ‘YAN TA’ADDAN KATSINA BA, SHASHANCI AKAI.

Spread the love

A Shekarae da ta Gabata 2019 Sakataren Gwamna Dr. Mustafa Inuwa ya Jagaoranci yin Sulhu da ‘Yan Ta’adda da Umarnin mai Girma gwamna.

A Zahirin Gaskiya Yin Sulhun bai Haifar da ɗ’a Mai Ido ba, duk da kuwa Sai da Aka Zauna da Shuwagabannin ‘Yan Ta’addan na Ɓangarori da yawa.

Ba Anan ta Tsaya ba, Mai girma Gwamna Yayi Ma Yan Ta’adda Shatara ta Arziki, An Jawo su a jika, Duk Bayan Wasu ‘yan Kwanaki ya Kan Gayyato su Domin Su Ƙara Bada Shawar-wari.

Bayan Wannan Sulhun da Fari An samu Sauƙin Yin Ta’addaci, Amma daga Baya Sai Aka Koma Gidan Jiya, Ta’ddanci Garkuwa da Mutane Satar Shanu Kashe-Kashe Da ƙone-ƙone ya Ƙaru.

Hakan Yasa Gwamna Yasaka Ma Talakawa Dokar Hawa Mashina Daga ƙarfe 7:00 Na Yamma Zuwa ƙarfe 6:00 Na Safe, Shin Saka Wannan Dokar ya yi Alfanu a wajen ‘yan Ta’adda, Wane Nasarori Aka Samu?.

Wannan Doka ta Hana Hawa Mashina Bata Shafi ‘Yan Ta’adda ba, Yan Gari Kaɗai ta Shafa, Domin Inda ‘Yan Ta’adda Suke Jami’ai Basu Zuwa, ‘Yan Ta’adda Suna Zuwa Ta’addanci Duk Lokacin da Suka Ga Dama, saka Doka ba ta Hanasu yin Ta’addanci ba.

‘Yan Ta’adda Suna Zuwa Su yi Ta’addanci Da Rana Gatse-Gatse Su Kashe Mutane Su Kwashe Masu Dabbobi Su Ƙwace Musu Dukikoyin su Su Yi Wa ‘Yan Mata Fyade Su Ƙone Masu Gidaje.

Me Yasa Gwamnati Yanzu Bata ba Tsaro Muhimmanci ba, Me Yasa Yanzu Hankalinta Ya Karkata Akan Corona-virus, Talakawa Da Ake Ma Wannan Aika-Aikar Basu San Corona ba, Ta’addancin da Ake Musu Shine Annobar su.

Me Yasasa Gwamna Yafi ba Corona Muhimmanci Fiye Da Ta’addanci?

Me Yasasa yadda Kullum Ake Fidda yawan Waɗanda Suka Kamu Da cutar amma Ba Za’a Fidda yawan Waɗanda Yan Garkuwa da Mutane Suka Kama ba?

Me Yasasa Yadda Kullum Ake Fidda yawan Waɗanda Cutar Ta Kashe amma ba Za’a Fidda yawan Mutanen da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe ba?

Me Yasasa yadda Kullum Ake Fidda Yawan Waɗanda Suka Warke daga Cutar amma Ba Za’a Fidda Yawan Waɗanda Aka Kuɓutar daga Hannun masu Garkuwa da Mutane ba?

Me Yasasa Idan Aka Kira Jami’ai a daidai Lokacin da Ake Ta’addanci Basu Zuwa da Wuri Sai Angama Amma Idan Aka Kira NCDC Cewa ga Masu Cuta Suke Zuwa Cikin Gaggawa?

ƙwarai Dole Su ba Corona Muhimmanci, Saboda Corona Batasan Talaka Ko Mai Mulki ba, Kowa Kamawa Take, tun A nan yakamata Talaka Yasan Ba Rayuwarsa Ake Karewa ba.

An kashe ma Wasu Iyaye An kashe ma Wasu Mataye Ankashe ma Wasu Mazaje Wasu Kuma Kuma ‘Ya’ya ye, Amma Har yanzu Bamuji Shugaban da yaje Yi musu Jaje ba.

Ashe Gwmnati tanada Ƙarfin da idan aka Zageta zata Kama Mutum Ayi Masa Hukunci, Amma Bazata Iya Kamo ‘Yan Ta’adda A yi Masu Hukunci ba.

Wai Menene Talakawa Suka yima Masu Mulki da Suke Gallaza Masu Azaba, Me Yasa Har yanzu Sunƙi Tashi Tsaye Domin a Kauda Ta’addanci, Me yasa ba Za’ai Wasu Sauye-Sauye ba Kasancewar Cin Hanci ya yi Yawa.

Wace Irin Lalacewa ce yin Sulhu da ɗan Ta’dda, meye yasa Ba za’a je Inda ‘yan ta’addan nan Suke a Gama da su ba tunda ansan Inda Suke, Talakawa Suna Kallon Mutanen da ke Cikin Gwamnati Waɗanda ake Zargin Sunada Hannu Dumu-Dumu a Cikin Ta’addanci.

*Munji Sakaren Gwamna yana Magana a Radio yana cewa “An sace mutane a hanya kaza Amma yasa ankarɓo su” Wannan wane kalar Mulki ne Wanda Za’a Sace Bayin Allah Gwamnati ko Wasu Mutanen Gwabnati tasa a amsosu, Wannan yana nuna Akwai Mutanen da basu so Kashe-Kashen ya ƙare Saboda Wani (Interest).

‘Yan Ta’adda Suna Zuwa da Rana gatse-gatse Su Kashe bayin Allah Su yiwa ‘yan Mata ƙanana fyade su kwashe musu dabbobi su ƙone musu Gidaje Su kashe maza Su kashe Mata Su kashe yara Wannan wane irin Bala’i Ne.😥

Talakawa da yawa Suna Hannun Masu Garkuwa da Mutane, ‘Yan Uwansu Basu da Halin Biyan Kuɗin Fansa Allah ne kaɗai gatansu, munsan Wasu Watanni da Suke Wuce Anyi Garkuwa da Surukar Gwamna ba ta daɗe ba Aka gaggauta Amsota Kuma Aka yi Ƙwaƙwƙwaran Bincike aka Gano Waɗand Sukai Garkuwa da Ita, Shi malam Talaka Allah ne Gatansa.

Daga Ƙarshe Muna Addu’a da Roƙon Allah Duk Mai Hannu a Cikin Kisan da Akewa talaka Allah Ya Tona Masa Asiri, Idan Mai Mulki ne Allah Ya ƙwace Mulkin Idan Neman Yake Allah Ka Hanashi, Talakawa da Ake Juya ma Tunani Suna kashe ‘Yan Uwansu Allah ka Shiryasu su Daina, Idan ba masu Shiryiwa Bane Allah Ka Gaggauta Ɗaukar Mataki Kansu.

Nuraddeen Mannir
15th, may 020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button