Shirye-shirye

Gaskiya ‘Yan Film Da Mawaka Sun Kaunaceni Lokacin Da Na Shiga Kannywood, Inji Jaruma Raliya Muhammad.

Spread the love

Ina So Na Zama Fitatciyar Jaruma A Masana’antar Fina Finan Hausa, Inji Jaruma Raliya Muhammad.

Jarumar wacce aka haifeta a cikin garin Birnin Gwari na Jihar Kaduna.

Ta yi karatun firamare (Primary) daga nan ta tafi kwatar kwashi tayi Sakandire (Secondry) bayan nan ta tafi Jihar Zamfara inda tayi Difiloma (Diploma) akan Mahalli (Environmental Health) a College of Health And Technology Tsafe.

Jarumar tana fitowa a Fina Finai, kuma mawaƙiya ce.

Ta ce tana son ta zama fitacciya a Masana’antar fina finai.

Raliya Muhammad ta ce gaskiya bata fuskacci wani ƙalu bale ba, domin kuwa Ƴan fim da Mawaƙa sun kaunaceta.

Kuma tana girmama kowa a masana’antar ta kannywood, ta ce hakan shine dalilin da yasa idan zata bi hanyar da bata dace ba suna ƙoƙarin maida ita hanyar da ta dace, saboda ita baƙuwace har yanzu a harkar Film.

Jaruma Raliya Muhammad ta ce ta godewa Allah da ya kawota wanan Masana’antar ta fim, domin fim ya yi mata komai.

Ta kara da cewa sanadiyar fim taje inda bata taba tsammanin zuwa ba, idan ta fito yara da manya kowa yana san ya ganta, ta zamto tamkar madubi, wannan ma nasarace acikin harkar sana’a.

Jarumar ta ce a yanzu haka akwai fina-finanta kusan guda biyu da take aikinsu, ba da jimawa ba za su fito.

Raliya Muhammad ta ce tana yiwa Masoyanta albishir, cewa fina-finanta na wannan karon sai sunfi wadanda suka kalla a baya.

Ta kara da cewa tana alfahari da Masoyanta, domin kuwa da su take takama.

Sannan ta ce ƙofa abude take ga mai son magana da ita, kaitsaye yaje shafina na Instagram ….real_raliya_m yayi mata magana ta DM Insha Allah zai sameta.

Jarumar ta roki matasa kowa ya kama sana’a, kada mutum ya raina sana’a koya take, domin kuwa ita sana’a tana hanin fadawa muguwar rayuwa.

Raliya ta fito a fina finai kamar haka
1-Raliya
2-Rayuwar Masoya
4- Babban rabo
5- Sanata
Tana waƙoƙi
1-Siyasa
2- Sarauta,
3- Da fina finai dana Aure.
Tana hawa waƙar Soyayya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button