Rahotanni

Gidaje Miliyan Goma ne Zasu Amfana Da Wutar Lantarkin Mambila — Shugaba Buhari

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya bayyana Cewar Da Zarar An Kammala Tare da Kaddamar Da Gidan Wutan Da Ake Gab da Kammalawa Na Mambila, to Kuwa Babu Shakka Gidan wutar Lantarkin Zai wadata akalla Gidaje Miliyan 10 Da Hasken Wutar Lantarki.

Shugaba Buhari Ya Bayyana Hakanne a Lokacin da yake Zantawa Da Manema Labarai Akan Yadda Ake Kokarin Shawo Kan Annobar COVID – 19 a Kasashen Afirka, Wanda Shine Shugaban Kwamitin yakar Cutar Na Kasashen Afirka.

Shugaba Buhari yakara Dacewar Kasashen Nahiyar Afirka Suna Gab Da Samun Cikar Burinsu a Bangaren Masana’antu Da Samar Da Kayayyakin Da Kasashen Suke Bukata, Inda Yakara Da cewar Najeriya Ta Samar Da Kamfanin Tace Danyen Man Fetur Mai Zaman Kansa, Wanda Shine Mafi Girma a Fadin Duniya, Wanda a Baya Kasar bata Iya Tace Man Fetur Din Da take Samarwa sai an Fita dashi Kasashen turai, wanda Su Suke tacewa Tare da Dawo Mana dashi.

Sannan ya Bayyana Kasashen Da Suke Kokarin Dawowa Da Najeriya Kudaden Ta Da wasu daga Cikin Tsofin Shuwagabannin Kasarnan Suka kwasa Tare da Jibgewa a Kasashensu, a Matsayin kawaye Ko ince Abokanan Mutuncin Najeriya.

Sannan ya godewa Kasashen a Bisa kokarinsu Na Hada kai Da Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button