Labarai

Gidan Radiyon RFI sun buga labarin mutuwar Sarauniyar ingila da Ayatullah..

Spread the love

Gidan rediyon Faransa RFI ya nemi gafara kan labaran ƙarya da ya ƴada na mutuwar shahararrun mutane kusan 100, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta Ingila da kuma fitaccen ɗan ƙwallon Brazil Pele.

Radio France International da ke yaɗa labarai a harsuna da dama ya wallafa labaran mutuwar ne a shafin Intanet.

Amma kafar ta ce matsalar na’ura ce ta sa aka wallafa labaran mutuwar fitattun mutanen.

Sauran waɗanda RFI ta wallafa cewa sun mutu, sun haɗa da tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter da Raul Castro na Cuba da kuma jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei.

Yawanci dai kafafen ƴada labarai kan tattara tare da shirya labaran mutuwar fitattun mutane domin wallafa su nan take lokacin da aka sanar da mutum ya mutu.

Kafar ta ce labarai sama da 100 aka wallafa kan kuskure kuma ba a shafin RFI kawai ba har da na abokan hulɗa da suka haɗa da Google da Yahoo.Article share tools

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button