Labarai

Gobara Ta Kone Na’urorin Tantance Masu Zabe A Jihar Ondo Gabannin zaben Gwamna A Jihar.

Spread the love

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya ta ce babban ofishinta ya ci wuta a jihar Ondo da ke kudancin Kasar Nan.

Gobarar ta faru ne jiya Alhamis da dare a ofishin hukumar inda kuma ta ƙkone na’urorin tantance masu zabe a cikin kwantenar da aka ajiye su.

Sanarwar da hukumar INEC ta fitar a shafinta na Twitter ta ce jami’an kashe gobara sun yi kokarin kashe gobarar lokacin da ta tashi amma hakan bai samuba.

Hukumar ta kuma ce tana gudanar da bincike domin gano musabbin tashin gobarar.

Gobarar dai ta kine na’urorin tantance masu zaben ne gabannin zaben gwamnan jihar da za’ayi kwanan nan.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button