Gobarar Tankar Mai Tayi Ajalin Mutane 23 a Lokoja.
Akalla mutane 23 ne aka tabbatar sun mutu wasu da yawa kuma suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai a safiyar yau Laraba a layin Felele na Lokoja babban birnin jihar Kogi.
Motoci sama da biyar ne suka kone kurmus a hatsarin da ya afku, kuma shaidun gani da ido sun ce wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da daliban kwalejin fasaha ta Kogi.
Da yake tabbatar da asarar rayukan ga gidan talabijin na Channels TV, kwamandan sashen na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kogi, Idris Fika ya ce an ciro akalla gawarwaki 23 daga cikin wutar.
Hatsarin ya afku ne bayan da wata babbar motar dakon kaya dauke da babban motar haya ta rasa yadda za ta shawo kanta sakamakon taka birki da ta yi kan wasu motoci biyar da ke tafe.
Shaidun gani da ido sun ce mai yiwuwa sama da mutane 50 ne suka mutu a gobarar, ciki har da wasu mazauna garin wadanda ke jiran hawa motocin kasuwanci ta bakin hanya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, akwai zaman dar-dar a yankin, bayan jami’an tsaro sun bar wurin, inda daliban Kwalejin Kimiyya da ke kusa da wajen ke nuna rashin amincewa da yawaitar hadurran a hanyoyin yankin.
Dangane da fashewar tankar, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya nuna kaduwa da alhini.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun sa, Onogwu Muhammed ya sanyawa hannu, gwamnan ya nuna juyayin sa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
“Abin bakin ciki ne matuka da jin labarin mummunan al’amarin Na, hasarar rayuka, motoci , kadarori da sauran abubuwa masu kima a gobarar tankar man,” in ji shi.
Gwamnan, ya bukaci daliban kwalejin fasaha ta jihar Kogi da su kwantar da hankulansu yana mai bayyana cewa yana cikin bakin cikinsu game da mutuwar wasu abokan karatunsu a cikin bala’in.
Ahmed T. Adam Bagas