Labarai
Gobe Kungiyar kwadago zata tsunduma Yajin aiki kan tsadar fetir da tsadar rayuwa ga ‘yan Nageriya.


Kungiyar kwadago tana Mai cewa Muna tunatarwa ‘yan Najeriya da su tanadi abincin da zasu ci, domin ba gudu ba ja da baya, a gobe Laraba zamu tsunduma yajin aiki mafi muni a tarihin Najeriya wanda sai baba ta gani, za kuma mu hada da zanga-zanga a duk fadin kasar ~ Inji kungiyar kwadago NLC.
Kungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin ne kan tsadar Man Fetur da tsadar rayuwa da talakawan kasar suke ciki. Kusan sau biyar, kungiyar tana yunkurin shiga yajin aikin tana fasawa, amma a wannan karon tace babu abunda zai dakatar da ita. Shin ko kuna goyon bayan su?
✍️ Comr Abba Sani Pantami