Al'adu

Gobe Litinin El-Rufa’i zai rantsar da sabon Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

Spread the love

Gwamna El-Rufai zai nada Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau Gobe Litinin.

Gwamna Nasir El-Rufai a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2020 zai naɗa Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

Wata sanarwa daga Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kaduna, Alhaji Ja’afaru Sani, ta ce Kwamitin Gudanarwa na nadin Sarkin Zazzau na 19, yana kira ga jama’ar Jihar Kaduna da ma ‘yan Najeriya baki daya da su fito gaba daya don tallafawa da kuma shaida wajan nadin Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarki na 19 na Zazzau da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i zai yi.

Sanarwar ta ce an kammala dukkan shirye-shirye don muhimmin abu kuma ba tare da jinkiri ba nadin zai gudana gobe Litinin 9 ga Nuwamba, 2020, a dandalin Muhammadu Aminu, Race Course GRA Zaria da karfe 10 na safe.

Sanarwar ta ce bayan nadin za ayi hawa na musamman, mai martaba Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, mambobin majalisarsa, Hakimai da masu rike da mukami a masarautar za su hau dawakai zuwa Fadar Sarki da ke Zariya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button