Gobe Litinin Kasar Saudiyya Zata Sanarda Matsayarta Kan Aikin Hajji.
Kasar saudiyya ta fitarda sanarwar cewa gobe Litinin zata sanarda matsayarta kan ko za’ayi aikin hajji a wannan shekarar, ko ba za’ayi ba.
Shugabannin kasar saudiyya sun kwashe lokaci suna nazari tare da dubar ko zai yuyi ayi aikin hajji a wannan shekarar, ko ba zai yuyu ba.
Wannan takaddama ta biyo bayan bullar annobar cutar Coronavirus a wasu sassan kasar.
Ministan harkokin addinai na kasar Saudiyya Sahib Zada Noor’ul-Haq shine ya bayyana cewa ranar Litinin 15 ga watan Yuni Gwamnatin kasar zata cimma matsaya game da yuyuwa ko rashin yuyuwar aikin hajji a wannan shekara.
Tuni al’ummar duniya suka fara addu’a tare da fatar ganin kasar saudiyya ta sahale ayi aikin hajji a wannan shekara.
Sai dai wasu na ganin cewa matakin bazai wuce amince da yin aikin hajjin ba, kasancewar kasar saudiyya ta kafa wasu kofofi da zasu taimaka wurin gano masu dauke da wannan kwayar cuta ta Coronavirus.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama