Labarai

Goyon bayan Fulani Jami’an tsaro sun cafke Shugaban Kungiyar Arewa Alh Nastura.

Spread the love

Da safiyar wannan ranar ta alhamis Shugaban Gamayyar Kungoyoyin Arewa cin Najeriya Alh Nastura Ashir Shariff tare da tawagarsa sun shirya yin Press Release a jihar Kaduna.

Wannan taron na manema labarai da kuma tattaunawa akan halin da Al’ummar Fulani da ma halin da Arewa cin Najeriya take ciki wajan Kashe-Kashe, Kidnapping, Yan Bindiga Dadi da sauransu.

Bayan isar tawagar jihar Kaduna domin gudanar da wannan tattaunawar Jami’an tsaro kimanin motoci uku sun farwa wannan tawagar tare da dakatar da yiwuwar taron, a dai dai lokacin kuma suka tafi da Shugaban Gamayyar da kuma President na Gamayyar kungiyoyin Balarabe Rufa’i.

Har kawo lokacin da muke hada wannan rahotan babu tabbacin inda aka tafi dasu inda muka zanta da wadanda abun ya faru gabansu, shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka kara da cewa farko anyi hanyar Zaria da Shugaban Gamayyar kuma ansake ganin sunyi hanyar cikin garin Kaduna dasu.

A dai-dai lokacin da Arewa take fama da halin ta’addanci tare da barazana daga yan bindiga dadi a wannan gabar kuma hukuma take kokarin dakatar da masu kokarin ganin ansamu daidaito da zaman lafiya tabbatacce a wannan yankin namu na Arewa.

A karshe Gamayyar kungiyoyin tayi kira ga Mahunkunta dasu gaggauta sakin Shugaban Gamayyar Alh Nastura da kuma wadanda aka kama a tare dashi baki daya batare da wani sharadi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button