Labarai

Gudauniyar Sanata Uba Sani ta shirya bawa matasa Horo Domin samun Rancen Milyoyin Naira daga CBN.

Spread the love

A wani yunkuri na zurfafa hada-hadar kudi da kuma samar da dama don samun damar mallakar guraben bayar da bashi ga mutanen yankin Kaduna ta Tsakiya, Gidauniyar Uba Sani tare da hadin gwiwar babban bankin Najeriya (CBN) sun shirya wani shiri na wayar da kai na kwana biyu ga masu ruwa da tsaki a fadin kananan hukumomi bakwai dayake wakilta.


Wannan taron ya samu halartar Shugabannin Kansiloli, Shugabannin Gundumomi, shugabannin addinai (wakilan JNI da CAN), jami’an Majalisar Matasa ta kasa (NYCN), shugabannin kungiyoyin nakasassu, shugabannin siyasa,

shugabannin matasa da mata a fadin kananan hukumomin bakwai na yankunan
Wannan shiri ya samo asali ne sakamakon dogon kokarin da mai gidauniyar  Sanata Malam Uba Sani Sani yakeyi na tabbatar da cewa jama’ar gundumar Sanatan ta Kaduna ta Tsakiya dama Arewa baki daya sun yi amfani da damar da Gwamnatin Tarayya ta ba su na Shirye-shiryen Tsoma baki a harkar ta Samun rancen. 


Ya lura cewa a cikin shirye-shiryen da suka gabata yawancin mutane ba za su iya amfana ba domin ba su da asusun ajiyar banki kuma ba su da masaniya ko kaɗan game da hanyoyin samun rancen. A Maimakon kawai ya nuna damuwa da halin rashin sanin hanyoyin Mai Girma Sanatan ya dauki matakai don magance lamarin, don haka  ya shirya  fadakarwar
Manufar Gidauniyar ita ce ta samu kusan mutane miliyan 1 da za su bude asusun banki tare da samun ilimin samun kudi a jihar Kaduna, sannan a samu mutane miliyan 4 a yankin Arewa maso Yamma su bude asusun banki ba tare da takura  ba.
Mahalarta taron sun yi godiya ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da kuma Uba Sani Mai gidauniyar kan daukar matakin da suka nuna da nufin sanya su a cikin kyakkyawan yanayi don cin gajiyar shirye-shiryen shiga tsakani na Gwamnati tare da sanya sucikin tsarin hada-hadar kudin. Sun yabawa Sanata Uba Sani musamman bisa hangen nesan sa da jajircewa wajan daukaka halinda mutanen da suke ciki ta hanyar basu kayan aiki da karfafa gwiwa.
Sa hannuAbubakar Rabiu AbubakarBabban jami’in yanki na mazabar dan majalisar dattijan Kaduna ta tsakiya.22, Disamba, 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button