Labarai
Gwabnatin Jahar Kano ta Haramta Goyo Akan Babur Mai kafa Biyu
Shugaban hukumar kula da sufurin Ababen Hawa A Jahar Kano (Karota) Dakta bappah babbba Dan Agundi yace Gwabnatin Jahar Kano ta Haramta Goyo Akan Babur daga ranar Alhamis 18 ga wata june dokar zata fara Aiki A duk fadin Jahar Kano
Dan Agundi yace dama Akwai dokar Hana goyo Akan babur da majalisar dokokin jahar Kano tayiwa doka inda ya bayyana andawo da dokar ne sakamakon ganin yadda Achaba take kokarin dawowa A kwaryar birnin Kano
Baffa Dan Agundi ya bayyana haka A jiya yayin da yake zantawa da manema labarai A hedikwatar hukumar karota dake Kano
Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano