Rahotanni

Gwama Tambuwal ya raba motoci domin yaki da yan ta’adda

Spread the love

Matsalar Tsaro, Gwamnatin Jahar Sokoto Ta Samarda Motocin Da Zasuyi Rangadi A Kananan Hudu Dake Jahar.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama
Gwamnatin Jahar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta Samarda Motoci da zasuyi shawagi a kananan hudu dake fama da matsalar a Jahar.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa Motocin zasuyi aikin ne na tsawo. Awanni goma Sha biyu a kowanne yini.
Kananan hukumomin da ke fama da matsalar Tsaro a Jahar sune, Isa, Rabah, Goronyo, dakuma Sabon Birni, kuma wadannan sune kananan hukumomin da Wadanda Motoci zasuyi Rangadi.
Haka Gwamnan ya tabbarda cewa Wadannan motoci zasuyi aiki daga karfe shidda na safiya, zuwa karfe shidda na Yamma a kowanne yini.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na musamman da aka shirya don magance matsalar Tsaro dake addabar Jahar.
Gwamna Tambuwal ya shawarci yan sanda, jami’an kiyaye hadurra, dakuma sauran al’ummar Jahar da su dunga yin gaggawa wurin mika korafinsu kan sha’anin Tsaro don kawo karshen bata Gari dake addabar Jahar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button