Labarai

Gwamanati Na Gina Tituna 331 A Karkara Cikin Kasafin Kudi Na 2021, Cewar Shugaba Buhari

Spread the love

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnagtin sa na gina tituna a karkara har 331 a fadin kasar nan.

Buhari ya bayyana haka da yake gabatar da kasafin kudi na 2021 1 zauren majalisa ranar Alhamis.

Ya kara da cewa wadannan hanyoyi da ake ginawa da gyara duk sai da aka tabbata hanyoyi ne da za su taimaka wa manoma.

Wasu daga cikin manyan hanyoyi da gewamnatin Buhari yi yanzu sun hada da titin Ilorin-Jebba-Mokwa-Birni Gwari, Lagos-Ibadan Expressway, Enugu-Onitsha da sauran su.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya gabatar da Kasafin Kudin 2021 a majalisar tarayyar Najeriya ranar Alhamis.

Buhari ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 13 kasafin 2021.

Gwamnati ta ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum. Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button