Labarai

Gwamantin Jahar Jigawa Ta Kara Sanya Dokar Hana Zirga-Zirga A Kananan Hukumomi Uku.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Gwamnatin jahar Jigawa wacce Malam Badaru Talamiz ke jagoranta ta umarci rufe kananan hukumomi uku bayan samun sabbin masu dauke da cutar Corona Virus.

Gwamnan yafadi hakanne yayin da yake gabatar da jawabi a yau Talata a gidan gwamnatin dake Dutsen jahar jigawan.

Mutanen da aka samu dauke da cutar su biyu na farko dan Gujungu ne dake karamar hukumar Taura, dayan kuma dan Birnin kudu ne Amma yana aiki a karamar hukumar Gumel.

Biyo bayan samunsu da cutar Gwamnan ya bada umarnin garkame kananan hukumomin guda uku domin tabbatar da rashin bazuwar ita wannan cutar a fadin jahar.

Muna roqon Allah yakiyaye Al’umma baki daya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button