Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf Ya Jajantawa Gwamnatin Jahar Borno Akan Bala’in Ambaliyar Ruwa

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika sakon jajen sa ga Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da gwamnati da kuma al’ummar jihar bisa mummunar ambaliyar ruwa da ta addabi mafi yawan yankunan Maiduguri sakamakon rugujewar Dam din Ala.

Haƙiƙa wannan mummunan lamari ya kasance mai ban tausayi da ban al’ajabi yayin da aka yi asarar rayuka da yawa, iyalai da al’ummomi da yawa sun rasa matsugunnansu yayin da aka sami asarar gidaje, kasuwanci da muhimman ababen more rayuwa.

“Zuciyarmu tana bakin ciki ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu ko suka jikkata da kuma da yawa da aka raba daga gidajensu. Mun fahimci zurfin tunani da tasirin tattalin arziki da wannan bala’i ya haifar, kuma mun tsaya cikin hadin kai tare da daidaikun mutane da iyalai da abin ya shafa.”

Don haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci al’ummar jihar Borno da su ci gaba da kasancewa da karfi da hadin kai a wannan lokaci mai matukar wahala, ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyi da sauran al’umma baki daya da su hada karfi da karfe wajen bayar da taimako da tallafi ga wadanda wannan bala’i ya shafa. .

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma baiwa duk wadanda wannan bala’i ya shafa ikon sake gina rayuwarsu.

Sa hannu:
BABA HALILU DANTIYE, MON, mni
Kwamishinan Yada Labarai
Jihar Kano
11/9/2024

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button