Labarai

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kotunan tafi da gidanka domin magance satar waya a Kano

Spread the love

Mista Yusuf ya ce an haska manyan titunan birnin bayan shafe shekaru takwas na duhu yayin da aka kashe fitulun.

Gwamna Yusuf Abba ya amince da kafa kotunan tafi da gidanka domin tabbatar da hukunta masu satar waya a jihar Kano cikin gaggawa.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce kotunan tafi da gidanka za su hada hannu da rundunar hadin gwiwa ta musamman domin gurfanar da mutanen da aka kama.

Mista Yusuf ya ce an haska manyan titunan birnin bayan shafe shekaru takwas na duhu yayin da aka kashe fitulun.

“Mayar da fitilun kan titi na cikin kokarin da sabuwar gwamnati ke yi na magance matsalar fashi da makami da sace-sacen waya da sauran miyagun ayyuka, musamman a babban birnin Kano.

“Aikin da ake ci gaba da gudanarwa ya fara tun ranar Talata kuma zai ci gaba har sai an kubutar da kowane bangare na jihar daga duhun da ke ba da mafaka ga masu aikata laifuka da ‘yan bangar siyasa,” in ji shi.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button