Gwamna Abba na Jihar Kano ya mayarda Yaran da aka sace ga Iyayensu.
Kimanin yara ‘yan asalin jihar Bauchi bakwai ne gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake ha’da iyayensu dasu a gidan gwamnatin jihar Kano bayan kubtar dasu daga masu satar Yara.
Gwamnan wanda ya bayyana hawayen jin dadin aikin da rundunar ‘yan sandan jihar Kano karkashin jagorancin CP Muhammad Hussain Gumel ta yi.
Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda ya yi mamakin gano yara bakwai da aka sace daga Bauchi ana sayar da su a jihohin Anambara da Legas, ya bayyana kaduwarsa kan ’yan kungiyar asiri da suka kware wajen sace-sace da fatauci da siyar da yara da kuma kananan yara daga jihohin Arewa.
Gwamnan ya yi kira ga iyaye da su zama masu lura da kuma kula da ‘ya’yansu.
Ya kuma yi kira ga dan uwansa gwamnan jihar Bauchi da ya dauki tsatsauran mataki na shari’a a kan wadanda ake zargin.
Gwamnan ya tuno da yaran Kano 11 da aka yi zargin an sace aka sayar da su a Anambra a shekarun baya.
Da yake mayar da martani kan lamarin, daya daga cikin iyayen yaran da aka sace Malam Saad daga Bauchi wanda yaronsa Abdulmutallif Saad ya ce ba su da kalmomin godiya ga gwamna da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane tara da ake zargi da satar daga Bauchi, wadanda aka kama a tashar mota ta Mariri da ke Kano a kan hanyarsu ta zuwa Legas.