Labarai
Gwamna Abba Ya kafa Kwamitin binciken Ganduje kan yadda ya kashe bilyan 10bn ba bisa ka’ida ba a karshen mulkin sa.
Gwamnan Kano Alh. Abba K Yusuf, ya amince da kafa kwamiti da zai bibiyi kudaden da gwamnatin baya ta kashe ba bisa kai’da ba a karshe wa’adin mulkin, wanda Adadinsu ya kai biliyan goma (10).
Wadanda aka kafa a kwamitin sun hada da:
- Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Hon. Musa Sulaiman Shanono
- Kwamishinan Shari’a, Barrister Haruna Isa Dederi.
- Kwamishinan Ilimi, Hon. Umar Haruna Doguwa.
- Kwamishinan Noma, Dr Danjuma Mahmood.
- Sakataren Gwamnati, Dr Abdullahi Baffa Bichi.
- Ahmad Garba Sale a matsayin Magatakardar Kwamitin.
Gwamnan ya kuma umarcesu dasu fara gudanar da aikin nan ta ke.