Gwamna Abba ya tsige Baffa Bichi da Sagagi Amatsayin Sakataren Gwamnatin da Shugaban ma’aikatan Gwamnatin sa.


A wata babbar shawara ta siyasa, gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya sanar da yin garambawul ga majalisar zartarwa ta jihar domin aiwatar da tsarin siyasar gwamnatinsa na gaskiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, gwamna Yusuf ya bayyana cewa an yi wa majalisar Jami’an sa garambawul
A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya ci gaba da cewa shawarar da aka dade ana jira ta zo ne don ba da damar gudanar da aiki mai inganci wanda zai samar da karin Samar da damar dimokuradiyya ga mutanen jihar Kano.
Wadanda babban sauyin ta shafa sun hada da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Alh. Shehu Wada Sagagi wanda yanzu ofishinsa ya ruguje, kuma sakataren gwamnatin jihar, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya sauka sakamakon matsalar fannin lafiya.
A cewar Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Yusuf ya tsige wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa, ya kuma sake nada wasu mukamai domin inganta ayyukan gudanar da mulki da na siyasa.
Wadanda suka koma kan mukaman su ne babban lauya kuma kwamishinan shari’a, Barr. Haruna Isa Dederi, kwamishinan noma, Dr. Danjuma Mahmoud, kwamishinan lafiya, Dr. Abubakar Labaran, kwamishinan kasa da tsare-tsare, Hon. Abduljabbar Mohammed Umar, kwamishinan kasafi da tsare-tsare Hon Musa Suleiman Shannon da kwamishinan ayyuka da gidaje Engr. Marwan Ahmad.
Sauran wadanda suka Ci gaba sa rike mukaman sun hada da kwamishinan albarkatun kasa da ma’adinai, Sefiyanu Hamza, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Ahmad Tijani Auwal, kwamishinan matasa da wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci, Adamu Aliyu Kibiya da na Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Mohammad Inuwa Idris Rtd.
Sanarwar ta ce, wadanda aka sake nada su ne mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulssalam wanda ya koma ma’aikatar kananan hukumomi zuwa kwamishinan Ilimi Mai zurfi na makarantu, Hon. Mohammad Tajo Usman ya koma ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu da kuma Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata daga kwamishinan Ilimi Mai zurfi na makarantu zuwa kimiyya da fasaha da kere-kere.
Sauran da ke cikin jerin sunayen da aka tura sun hada da Hon. Amina Abdullahi daga ayyukan agaji da rage radadin talauci zuwa ma’aikatar mata da yara da nakasassu, Hon. Nasiru Sule Garo, daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman.
Kwamishinan sa ido da tantance ayyukan Hon. Yanzu Ibrahim Namadi ya koma ma’aikatar sufuri, yayin da Hon. Umar Haruna Doguwa na ma’aikatar ilimi ya koma ma’aikatar albarkatun ruwa.
A cikin jerin sunayen da aka sake sanyawa, akwai Hon. Ali Haruna Makoda ya koma Ma’aikatar Ilimi, Hon. Aisha Lawal Saji daga ma’aikatar mata, yara da nakasassu zuwa yawon bude ido da al’adu, da Hon. Muhammad Diggol daga sufuri zuwa ma’aikatar sa ido da tantance ayyukan.
A halin da ake ciki, Gwamna Yusuf ya kori mambobin majalisarsa guda biyar da suka hada da Ibrahim Jibril Fagge, na ma’aikatar kudi, Ladidi Ibrahim Garko, al’adu da yawon bude ido; Baba Halilu Dantiye, Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Shehu Aliyu Yammedi, Ayyuka na Musamman da Abbas Sani Abbas, Ci gaban Karkara da Al’umma.
Haka kuma, Gwamnan ya umurci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da kwamishinoni biyar da aka sallama da su kai rahoto ofishin gwamnan domin yiyuwar a sake nada su.