Gwamna Badaru Mai mala Buni Nason Jonathan ya fito takara a APC
Wasu gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da shugabannin jam’iyyar sun ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, yayin da matsin lamba ke ci gaba da matsa masa kan ya tsaya takarar zaben 2023.
Sun ziyarci Jonathan ne a gidansa da ke Abuja don taya shi murnar cika shekara 63 da haihuwa.
Wadanda suka ziyarci tsohon shugaban sun hada da: Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru.
Hakanan tsohon shugaban majalisar dattijai, wanda jigo ne a jam’iyyar APC, Ken Nnamani, yana cikin ziyarar.
Ba a dai sani ba idan jiga-jigan APC sun gabatar da bukatar Shugaban kasa ga Jonathan a yayin ziyarar.
Jonathan, wanda ya yi wa’adi daya bayan kammala wa’adin mulkin marigayi Shugaba, Musa Yar’Adua ya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a 2015.
Duk da haka, a ‘yan kwanakin nan ana ta kiraye-kiraye ga Jonathan ya tsaya takarar karshe a matsayinsa na shugaban kasa bayan Buhari a 2023.