Gwamna Badaru ya bayyana dalilin da yasa APC zata iya faduwa a zaben 2023.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na iya faduwa zaben 2023 a jihar idan ba a duba rikicin jam’iyyar ba.
Badaru ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin rikon jam’iyyar APC a Duste, babban birnin jihar, a ranar Juma’a.
Ya yi gargadin cewa ba zai kara yarda da duk wani dan jam’iyyar da ke cudanya da bangarori a jihar ba.
Kaddamar da kwamitin na zuwa ne bayan an cire Habibu Sara, tsohon shugaban jam’iyyar APC a Jigawa daga mukaminsa bayan taron tattaunawa.
An zargi Sara da yin biyayya ga Sabo Nakudu, Sanata mai wakiltar Jigawa ta tsakiya.
“Idan muka bari son zuciyarmu ya yi tasiri a kan bukatunmu na gama kai, ina tabbatar muku za mu yi asara kuma a lokacin wa’adina ya wuce.
“Mu ne mambobin jam’iyyar da ke da alhaki, na taba sadaukar da dan takarar gwamna na ga masarautar Hadejia domin a samu zaman lafiya. Duk da haka, daga baya Allah ya sanya ni gwamna, ”in ji Badaru.