Labarai

Gwamna Dauda Lawal ya rage yawan ma’aikatun gwamnati 28 na Zamfara zuwa 16

Spread the love

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Zamfara ya sanya hannu kan dokar rage ma’aikatu a Zamfara daga 28 zuwa 16.

Gwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar rage ma’aikatun jihar Zamfara daga 28 zuwa 16.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin sa Nuhu Anka ya fitar.

Gwamnan ya bayyana cewa dalilin sake fasalin ma’aikatu da hukumomin gwamnati shi ne don rage tsadar tafiyar da harkokin mulki da inganta samar da ayyuka masu inganci.

Sanarwar ta ce “Sake fasalin shi ne tabbatar da aikin ceton gwamnatin Lawal a jihar.”

Sake fasalin zai kuma shafi sauran ma’aikatun gwamnati, hukumomi da ma’aikatun gwamnati da nufin tabbatar da inganci, aiki da kuma kaucewa sake aiki.

Mista Lawal ya tabbatar da cewa za a nada mutanen da suka tabbatar da gaskiya da aiki tukuru a ma’aikatu domin inganta harkokin gudanar da mulki da zai bunkasa jihar.

Sanarwar ta ce “Manufar sake fasalin za ta samar da karin damammaki da samar da karin ayyukan yi ga ‘yan kasa da kuma karfafa ayyukan gwamnati,” in ji sanarwar.

Don haka gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya.

“Ya kamata jama’ar mu su kuma ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar,” Gwamnan ya kara da cewa.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button