Gwamna Dikko radda Ya fitar da Naira Milyan 364.8m domin biyawa daliban katsina ku’din Jarabawar WA’EC.
Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Radda, ya amince da fitar da naira milyan 364, 842,000 domin biyan kudaden hukumar jarrabawar Afrika ta Yamma (WAEC) na kimanin ‘yan jihar Katsina mutun dubu 20,269.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan (CPS) ya fitar ta bayyana cewa daliban su ne wadanda suka zana jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2023 (WASSCE).
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan tun bayan hawansa mulki, ya sanya ilimi a gaba, kuma ya kuduri aniyar gyara tsarin ilimin firamare da sakandare da kuma manyan makarantun jihar.
Daya daga cikin manyan ajandar gwamnatin Gwamna Dikko Radda da wasu da dama shi ne na mayar da bangaren ilimi na jihar Katsina matsayi.
“Kuma mai girma Gwamna, tun hawansa mulki, ya nuna kwakkwaran jajircewarsa wajen gyara tsarin ilimin firamare da Sakandare da na Sakandare na Katsina.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Amincewar da ya bayar a yau kan makudan kudade sama da Naira miliyan 364 da za a yi amfani da su wajen daidaita kudaden daliban Katsina da bai gaza 20,000 na WAEC ba, ya bayyana hakan ne a kan irin kishin da mai martaba yake yi wa matasan Katsina da kuma bunkasar karatunsu.