Kungiyoyi

Gwamna El Rufa’i da matarsa sunyi taro Kan fyade

Spread the love

Biyo bayan gama gyaran dokar manyan laifuffuka ta 2017 mai lamba ta 5 sashe na 258 da majalissalar dokokin Jihar Kaduna ta yi, gwamna ya sanya hannu, wacce ta tanadar da hukunci mai tsauri na kisa tare da dandaƙa ga masu aikata laifin fyaɗe a Jihar Kaduna;

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i tare da Uwar Gidansa, Hajiya A’isha Ummi Garba Ahmad El-Rufa’i sun yi taro tare da dukkan manyan jagororin yaƙi da matsalar ta fyaɗe domin tattaunawa kan yadda za a cigaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su tainaka wajen magance matsalar ta fyaɗe gabaɗaya musamman ma cin zarafin mata da yara ƙanana.

A cikin jawabin da ya gabatar a ya yin taron, gwamna El-Rufa’i ya yabawa uwar gidan nasa Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i bisa goyon bayanta da ƙoƙari da jajircewarta kan fafutukar ƙwato ƴanci da ba da kariya ga mata da yara ƙanana waɗanda aka ci musu zarafi ta hanyar lalata.

Daga nan gwamnan ya ƙara da yabawa ma’aikatar ayyukan al’umma da samar da cigaba dangane da ayyukansu na yaƙi da dukkan wani cin zarafi da kyautata rayuwar al’umma haɗi da ƙoƙarin kawo ƙarshen fyaɗe da cin zarafin jinsi.

Baya da haka, gwamna El-Rufa’i ya kuma yabawa hukumomin duniya da ƙungiyoyin sa kai a cikin gida da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da su ke bayarwa wajen yaƙi da matsalar fyaɗe da cin zarafin ɗan adam a Jihar Kaduna.

Daga ƙarshe gwamnan ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na cigaba da yin duk mai iyuwa wajen ba da goyon baya domin ganin an kawo ƙarshen matsalar tare da tabbatar da hukunci ga duk waɗanda aka kama da aikata laifin.

Ita ma a nata jawabin, uwar gidan gwamnan, Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i ta yabawa dukkan ƴan gwagwarmaya masu fafutuka wajen yaƙi da matsalar. Daga nan ta kuma ƙara da jan hankalinsu da su cigaba da haɗa kai su kauda duk wani saɓani da bambance-bambance a tsakani domin ganin an magance duk wani nau’in cin zarafi da lalata rayuwar ƴaƴa mata da yara ƙanana a Jihar Kaduna. Inda daga ƙarshe kuma ta hore su da su cigaba da tafikar da aikinsu bisa tsari da ƙwarewa.

Mahalarta taron sun haɗa da:

  1. Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i
  2. Uwar gidan gwamna, Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i.
  3. Lauyar gwamnatin Jiha, A’isha Dikko
  4. Kwamishin ayyukan al’umma Hafsat Mohammed Baba
  5. Shugabar shirye-shirye na (UNFPA) na shiyar Arewa maso Yamma, Maryama Darboe.
  6. Shugabannin manyan ƙungiyoyin sa kai masu fafutukar kawo ƙarshen matsalar fyaɗe da cin zarafin al’umma a Jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button