Labarai

Gwamna El Rufa’i Da Sanata Uba Sani sun kafa Tarihi a jihar kaduna…

Spread the love

Batun harkar lafiya Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya yace Wa’adin mulkin Malam Nasiru El Rufa’i Na Farko Ya Cimma nasarar kafa Kyakkyawan Tarihi ta Hanyar Gina Cibiyoyin Kula da Lafiya (primary Healthcare Center) sama da dari biyu da hamisin 250 a jihar ta kaduna a yanzu Haka. domin bawa harkar lafiya mahimmanci Sanata uba Sani Shima a nasa bagaren ya bayar da Gudummawar Kayan Agaji da Kayan aiki zuwa ga wani sashi na hukumar wutar lantarki PHCs. Sanatan ya aminta da Shirin jagoranci Samar da filayen Fara wani aiki na Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Kasa (National primary Healthcare development Agency) wanda za ta aiwatar a wani sashi da sanatan ke wakilta, Waɗannan Ayyuka Idan aka zartar da su, Za su tafi ne Kai tsaye don inganta Cibiyoyin Lantarki na hukumar PHCs da ke yankin mazabun sanatan haka Kuma zai ƙarfafa wasu sashi sashi na Ma’aikatan Lafiya.

Cutar CoronaVirus COVID-19 cutace wacce ta Girgiza Tattalin Arzikin Duniya Haka Kuma ta saka wani yanayi Mai tsanani ga Cibiyoyin Kiwon Lafiyar Najeriyar. Abin sha’awar anan shine Motsi na Farko da Sanata Uba Sani Yayi shine cikin gaggawa ya dauki nauyin gabatar da kudri a Majalisar dattijan ta kasa a watan Yulin 2019, ya bukaci Majalisar Dattawan da ta umarci kwamitin ta na kiwon lafiya tare da Babban Daraktan Cibiyar hana yaduwar Cututtuka na hukamar (NCDC) akan Cimma Matsaya Na dokar Samar da Cibiyoyin Yanki yanki (Zones) A Duk Yankunanmu shida da Muke dasu a Nageriya tare da Samar da Ofisoshi A Duk Jihohin Tarayyar Nageriya kudrin na Sanata uba sani Wanda tuni Majalisar Dattawan ta zartar dashi ta kuma yanke shawara cewa ya kamata a samu kari cikin kasafin kudin don Gudanar da aikin hukumomin na NCDC da NPHCDA don basu damar cimma burinsu na na kawo karshen cutattukan, Bugu da kari Sanata Uba Sani ya dauki nauyin wani Kudurin domin Samar da Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya a Rigasa kaduna, (Federal medical Center Rigasa kaduna) Wanda Yanzu Haka kudrin Yana Majalisar ana Kan bin ka’idojin Rahotan yarjewa…

Burin Sanata Uba sani Shine kawo karshen matsalolin jihar kaduna dama Arewacin Nageriya baki daya sanatan ya rubuta wannan Labari ne Acikin littafinsa na cika shekara Daya a Majalisar dattijan Nageriya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button