Labarai
Gwamna El rufa’i ya bayarda umarnin Bude makarantun jihar kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da ranakun komawa makarantu, kwanaki kadan bayan da wasu jihohin suka koma Makarantu gadan-gadan.
A daren yau Laraba ne Gwamnatin ta fitar da sanarwar, wanda Al’umma suka dauki haka a matsayin bazata.
Gwamnatin ta bayyana ranakun 18 da 19 na wannan watan na Okyoba a matsayin wanakin komawa makarantun.
Sai dai ba gabaki daya makarantun zaa koma ba, yan aji 6 na makarantar Firamari da yan aji biyar SS2 na makarantun sakandare da yan aji biyu JSS2 na makarantun karamar sakandare ne zasu koma a makon gobe.
Makwanni biyu baya, Yan JSS 1 da yan SS1, suma zasu bi sahun dalubai wajen koma makarantun.
Rahotan bai bayyana ranakun da daluban Nazare da Firamari zasu koma makarantu ba. DIMOKURADIYYA: