Labarai
Gwamna El-rufa’i Zai ‘Kirkiri Karin masarautu biyu A masarautar Zazzau
Alamu sun bayyana cewa shirye-shiryen da gwamna Nasiru Elrufai keyi na kirkirar karin masarautu daga cikin
masarautar Zazzau.
Wannan na zuwa ne bayan ya gaji da duk kokarin da aka yi na shawo kan sarakunan su ba abokinsa Ahmed Nuhu Bamalli, ya zama magajin marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris.
Masarautun sune da za’a kirkiro sun hada da Kaduna, Zaria da Kudan.
Tuni aka shirya wani daftarin kudiri na kwaskwarimar dokar (Emirate da Chieftaincy) don gabatarwa gaban Majalisar Jiha don ci gaba.
Idan har aka tabbatar da kudirin, Magajin Garin Zazzau zai zama Sarkin Kaduna, yayin da Yarima zai kasance Sarkin Zariya ,dan Iya Aminu a matsayin Sarkin Kudan. Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano