Labarai

Gwamna El’rufa’i Ya Maka Wani Pastor A Kotu Domin Yace Masa Bazai Taba Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Jagorancin El’rufa’i ta maka pastor Abiodun Ogunyemi, Bishop na Cocin Anglican Communion Zaria a kotu, Bishop din dai yayi magana cewa gwamnan jihar kaduna Nasir El-Rufa’i, ba zai taba zama Shugaban Najeriya ba.

Ogunyemi ya yi wannan furucin ne a watan Nuwamban shekarar 2019 a kan rushe majami’u coci coci a jihar ta Kaduna. A lokacin ya ce ya kamata gwamna ya daina kunyata kansa tare da rushe majami’u a kowane bangare na jihar Kaduna,
tare da lura da cewa duk wani yunkuri na rusa shagunan ko kadarorinsu a Kasuwar Sabongari wannan mugunta ce, domin wannan mummunan aiki ne, kuma muguta ne kuma zai kasance yana da alaƙa da fushin Allah.

Hakanan Paston yace “Ya kamata gwamna El’rufa’i ya sani cewa ba zai taba zama Shugaban Najeriya ba. Yace ina wannan magana ne ta hanyar annabci a matsayin bawan Allah mai rai,” in ji bishop.

Ogunyemi ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kaduna kan tuhume-tuhume da ake yi a kan keta da aikata laifukan, karya da kuma ba da tsoro, in ji jaridar TheCable.

Pastor din dai Ya ce shi bai yi laifi ba game da tuhumar da ake yi masa, kuma kotu ta ba da belinsa. Alkalin kotun ya dage karar zuwa 28 ga Oktoba, 2020, don ci gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button