Labarai

Gwamna Ganduje zai ginawa malamai gidaje dubu biyar 5,000 a jihar Kano.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta gina rukunin gidaje dubu biyar 5,000 ga malamai a makarantun firamare da sakandare a jihar.

Manufar shirin ita ce samar da “matsuguni na dindindin” ga malamai da danginsu don kar su zama marasa muhalli bayan ritayarsu, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a karshen mako Nan.
Gwamnan ya bayyana shirin, wanda ake kira ‘Teachers Reserve Area (TRA), wanda gwamnatin jihar za ta aiwatar tare, da Gidauniyar Gidajen Iyali, da kuma Bankin Mortgage na Tarayya.

Da yake magana kan shirin da aka tsara yayin taron masu ruwa da tsaki a gidan Gwamnatin jihar ta Kano, Ganduje ya bayyana cewa kananan hukumomi 36, wadanda suke karkara, za su sami rukunin gidaje 100 kowannensu.

Kananan hukumomi guda takwas zasu sami rukunin gidaje 150 kowannensu. Akwai kananan hukumomi 44 a Kano.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar za ta samar da filaye da sauran kayan more rayuwa kamar wutar lantarki, ruwa, da hanyoyi yayin da sauran bangarorin za su kula da su.

Gwamnan ya nuna cewa shiga cikin shirin, wanda zai fara a watan gobe, na zabi ne kuma masu cin gajiyar dole ne su biya gidajen, kodayake, a cikin sauki.

“Gwamnati na ta damu game da tabbatar da araha da kuma samun gidajen malamai don kada su kasance cikin kunci idan sun yi ritaya daga aiki,” in ji Ganduje
Wata sanarwa da Darakta-Janar na Gidan Gwamnatin, Media da Hulda da Jama’a, Ameen Yassar ya ce, kwamitin kwararru, a karkashin jagorancin Daraktan Kula da Manufofi da Aiwatar da Manufofi, Alh. Rabi’u Sulaiman Bichi, an kafa shi ne domin ya fitar da hanyoyin da za su dace don aiwatar da tsarin gidajen malamai yadda ya kamata.

Alh. Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanar da aikin, ya ce shirin samar da gidajen malamin zai taimaka wa Dokar Ilimi kyauta a Jihar Kano.

Ya tuna cewa lokacin karshe da aka gina wa malamai gidaje a Kano shi ne a zamanin Hukumar Native.

Bichi ya ce gwamnatin jihar za ta samo karin kudade daga cibiyoyin hada-hadar kudi na tarayya don aiwatar da aikin.

Wakilin Gidajen, Engr. Musa Shu’aibu Mukhtar ya ce aikin zai samar da ayyukan yi, baya ga samar da ingantattun masaukai ga malamai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button