Gwamna ganduje zai Sulhunta rikicin apc
Gwamna Ganduje Zai Jagoranci Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo……
Kwamitin rikon kwarya na Jam’iyar APC Karkashin H.E Mai Mala Buni ya nada Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban tawagar Jam’iyar na kasa da zaiyi gangamin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo.
A ranar 19 ga watan Satumba mai zuwa ne za’ayi zaben Gwamnan Jihar ta Edo.
Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren Jam’iyar APC na kasa Yekini Nabena ya fitar, tawagar yakin neman zaben Gwamnan Jihar ta Edo zata kunshi karin Gwamnonin Jam’iyar masu ci guda 4 da mataimakin shugaban majalisar dattawa da tsoffin shhugabannin Jam’iyar 2.
Zaayi bikin Kaddamar da Kwamitin a ranar litinin 6 ga watan yuli insha Allah a shedikwatar Jamiyyar APC ta Abuja.
daga shafin Abubakar Aminu Ibrahim
SSA Social Media, Kano.