Tsaro

Gwamna Masari Ya Jawo Hankalin Burutai Shi Kuma Sarkin Daura Ya Jinjinawa Burtai….

Gwamnan Jahar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari yayi kira ga Hafsan Hafsoshin Kasar Nan Laftanar Tukur Yusuf Burtai, Kan Ya Kara Kaimi Wajen Ceto Rayuwar Al’ummar Kauyuka daga Yan Ta’adda.

Masari yace Kauyuka 8 Dake makobtaka da Dajin Rugu Suke Fama da Matsalar Yan Ta’adda.

Masari yace An Samu Sauki yanzu Amma Burtai Ya kara Motsa Sojojin Domin Kawo Karshen Yan Ta’addan Dake Addabar su a Yankin.

Shikuwa Sarkin Saura Da Burtai Ya Ziyarceshi a Fadarsa Mai Martaba Sarkin Dauran Alhaji. Dr. Umar Faruq Umar Cewa Yayi Ya Jinjinawa Gwarzon Sojan Bisa Irin Namijin Kokarin da Jami’ansu Keyi a Kokarinsu na Murkushe Ta’addanci a Fadin Jahar.

Burtai din ya ziyarci Jahar Katsina ne a Kokarinsa na Inganta Tsaro A Jahar.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button