Labarai

Gwamna Matawalle Na Zamfara Ya Bada Hutun Kwanaki 3 Dan Jimamin Masoyansa Da Suka Rasu A Hadarin Mota.

Spread the love

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa gwamnatin jihar ta sanar da kwanaki 3 a matsayin ranekun hutu dan a yi jimamin masoyansa da dama da suka mutu a hadarin mota tsakanin hanyar Funtua zuwa.

Masoyan na gwamnan sun taru ne inda suka shiga tawagarsa suna masa maraba da dawowa daga Abuja inda mota da rahotanni suka bayyana cewa ta kamfanin Dangote ce ya yi taho mu gama dasu.

Kakakin gwamnan, Zailani Baffa ya bayyana cewa a lokacin da lamarin ya faru gwamnan ya wuce wajen amma yasa aka dawo da baya sannan kuma ya bada umarnin kwashe gawarwakin wanda suka rasu din aka kaisu Asibitin Yariman Bakura na jihar. Washe gari gwamnan da Mukarrabansa sun hadu inda aka yi jana’izar mamatan tare dasu.

Ya bayyana cewa a lokacin jimamin na kwanaki 3 za’a yi kasa-kasa da tutar Najeriya dan girmamawa ga mamatan.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button