Tsaro
Gwamna Tambuwal Ya Hidimtawa Sojoji.
Gwamnatin Sokoto Ta Baiwa Sojoji Mashin Boxer guda 50 Domin Inganta Tsaro a Jahar.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya Rabawa Sojojin Yankinsa Mashin Babur Kirar Boxer guda 50 Domin Shiga Lungu Da sakon Na Jahar.
Sakataren Gwamnatin Jahar Malam. Saidu Umar ne Ya Mika Mashinan ga Kwamadan Sojin Bataliya ta 26 dake Sokoto.
Kwamandan Sojan Kanar. Umar Ahmad Muhammad Ne Ya karbi Mashinan, San Nan Ya jinjinawa Gwamnan Da Irin Jajidcewar da Gwamnan Yakeyi Domin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jahar.
Kanar din Ya Bada Tabbacin Nan Bada Dadewaba Za’a kawo Karshen Yan Ta’addan da Suka Addabi Yankin Inji Shi.