Labarai
Gwamna Uba sani na Kaduna ya zama gwamnan farko daya fara biyan Albashin ma’aikata a cikin sabbin Gwamnoni.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da biyan albashin ma’aikatan jihar Kaduna da ma ‘yan fansho na watan Yuni 2023.
Akanta Janar na jihar Mrs Shizzer Nasara Bada ce ta bayyana hakan, inda ta ce, an amince da biyan Albashin watan Yuni na 2023 tun a ranar 21 ga watan Yuni, 2023.
Wannan shine karon Farko da Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba sani ya fara biyan Albashin tun bayan rantsar dashi a watan Daya gabata na Mayu wannan Kuma wata alamace Dake nuna cewa Gwamnatin Uba sani ba zata yi wasa da Albashin ma’aikatan Gwamnatin Jihar ba.