Labarai
Gwamna Uba sani Ya Na’da sani Kila amatsayin Shugaban ma’aikatan jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani ya amince da nadin Mr Sani Kila amatsayin sabon shugaban ma’aikata, Shugaban Ma’aikatan Ya kasance Kwararre Tsohon Jami’in kula da shige da fice ta Kasa Immigration.
Ya kasance tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Jihar Kaduna Kafin a turashi jihar Kano.
Sani Liman Kila ya yi karatun digiri na farko a fannin Turanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sannan ya yi digiri na biyu a fannin Kimiyyar Zaman Lafiya da magance rikice-rikice daga Jami’ar Open University. Ya halarci kwasa-kwasan da dama a fannin Gudanar da Jagorancin Jama’a da Gudanar da Ayyuka.
Mr Sani Kila ya kasance na hannun damar Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba sani na tsawon lokaci sama da shekaru talatin.